in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Algeria za su inganta hadin kai a bangaren fasahar sararin samaniya
2018-04-03 10:04:58 cri

Kasar Sin ta ce tana sa ran inganta hadin kai da Algeria a fannin fasahar sararin samaniya.

Mataimakin babban manajan hukumar kula da harkokin kimiyya da fasaha da suka shafi sararin samaniya Yang Baohua, ya ce kasar Sin na sa ran samun ingantaccen hadin kai a wasu ayyukan da za su biyo baya da suka shafi bangaren.

Yang da wasu wakilan kasar Sin da na hukumar kula da sararin samaniya ta Algeria, na daga cikin wadanda suka halarci bikin fara shawagin tauraron dan Adam na Algeria na farko wato Alcomsat-1 a ranar Lahadin da ta gabata.

An harba Alcomsat-1 ne daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Xichang dake kasar Sin a ranar 11 ga watan Disamban bara. Daga bisani, bangarorin biyu sun gudanar da bincike tare da nazarin shawagin tauraron.

Algeria za ta yi amfani da tauraron Alcomsat-1 da aka tsara zai yi shekaru 15, domin yada labarai da shirye-shiryen talabijin da sadarwar gaggawa da karutu daga nesa da tsarin intanet mai sauri da kuma tantance wurare.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China