Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a babban birnin kasar Guinea, Conakry, Boniface ya ce, kasar Sin ta samarwa kasashen Afrika damammaki wadanda a lokacin baya basu da su.
Kasar Sin tana cigaba da zama babbar mai ruwa da tsaki ga cigaban Afrika, ya kara da cewa, a da akwai wani nau'in mulkin mallaka wanda kasashen yamma ke yiwa Afrika, kuma shigowar kasashen Sin, Brazil da Japan ya karya wannan tsarin mulkin danniya a Afrikar.
Boniface ya ce, jarin da Sin ta zuba a Afrika ya samar da kyakkyawar makomar cigaba mai yawa, da suka hada da gina kayayyakin more rayuwa, gina filayen wasanni da dai sauransu.(Ahmad Fagam)