Jakada Shi ya ce tashar binciken sararin samaniyar( CSS) ba ta kasar Sin kadai ba ce, tasha ce ta duniya baki daya. Don haka dukkan kasashe ba tare da la'kari da girma ko matsayin ci gabansu ba, na iya shiga a hada gwiwa da su ba tare da nuna wani bambanci ba.
Bugu da kari, hukumomin gwamnati da masu zaman kansu dake da sha'awa ciki har da cibiyoyin bincike da masana da jami'o'i da kamfanoni masu zaman kansu masu nasaba da harkokin kimiya, suna iya gabatar da fannonin da za su yi hadin gwiwa da hukumar zartarwas tashar ta CSS,ko ta fannin yadda za a bunkasa tashar ko masaukin 'yan sama jannatin.
Ya ce, a matsayinta na kasa mai tasowa, a shirye kasar Sin ta ke wajen taimakawa sauran kasashe ta yadda za su kara karfin fasahar gina tashar binciken sararin samaniyarsu, musamman fannin binciken sararin samaniya.
A shekarar 2019 ake fatan kaddamar da tashar,kana a fara aiki da ita kadan-kadan a shekarar 2022.(Ibrahim)