in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta karyata zargin da Amurka ta yi mata game da kwaikwayon fasaha
2018-05-29 09:31:03 cri
Jakadan kasar Sin a hukumar cinikayya ta duniya (WTO) Zhang Xiangchen ya yi watsi da zargin kasar Amurka cewa, kasar Sin ta keta ka'idojin hadin gwiwa wajen yin satar fasaha, yana mai cewa, Amurka na daya daga cikin kasashen da ke sahun gaba wajen cin gajiyar sayar da fasahar.

Zhang ya bayyana hakan ne yayin zaman hukumar sasanta rigingimu na hukumar(DSB) biyo bayan zargin da Amurkar ta yi cewa, manufofin kasar sun samar da wata doka dake kare tattalin arzikin kasar ta yadda za su tilastawa kamfanonin ketare baiwa kamfanonin kasar fasahohinsu.

Jami'in na kasar Sin ya ce, musayar fasahar daga kamfanonin kasar Amurka zuwa kasar Sin ba wani bakon abu ba ne. Domin suna yi ne ta hanyar sharuddan kasuwanci da suka amince da su, kuma musayar sun dace da aniyar kamfanonin.

Jakadan na kasar Sin ya kuma lura da cewa, kasar Amurka ce ta fi kowa ce kasa cin gajiyar wannan tsari, yayin da kasar Sin a matsayinta na kasa mai tasowa, tana daga cikin kasashen da ke shigar da fasahohi daga kasar Amurka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China