Ma ya bayyana hakan ne yayin taron da kwamitin sulhun majalaisar ya kira don tattauna sabon fadan da ya barke. Ya ce kasar Sin tana sa-ido kan halin da ake na baya-bayan a yankin, kuma ta damu musamman game da hadarin tsanantar yanayi a yankin na Gaza
Jami'in na kasar Sin ya ce kasarsa na fatan sassan da abin ya shafa za su kwantar da hankulansu, su dakatar daukar duk wani mataki na soja kana su dauki kwararan matakan da za su rage zaman tankiya.
Ko da yaushe kasar Sin na kira da a daidaita rikicin Palasdinawa da Isra'ila ta hanyar tattaunawar lumana, kana bata goyon bayan tashin hankalin da zai kai ga ta'azzara yanayi har ma ya shafi fafaren hula.
Ma ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su ci gaba da tsayawa ga manufar warware wannan batu ta hanyar kafa kasashe biyu, kana su yi aiki kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada. (Ibrahim)