in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci shirin samar da ci gaba na MDD ya rika lura da bukatun kasashen da yakewa aiki
2018-06-01 20:30:47 cri

Wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya yi kira da a rika kiyaye martabar kasashen da ake gudanar da shirin samar da ci gaba na MDD a cikin su.

Ma Zhaoxu ya bayyana wannan bukata ne ga zauren MDD a jiya Alhamis, bayan da zaman ya amince da wani kudurin doka, wanda ke kunshe da kara kyautata ayyukan samar da ci gaba da MDDr ke aiwatarwa a kasashe daban daban.

Kudurin ya amince da kara martaba kasashen dake amfana da wadannan ayyuka musamman daga jami'an tsare tsaren shirin, wajen ba da jagoranci. Kaza lika ya bayyana irin ikon da kasashen ke da shi, na mallakar 'yancin su, ta yadda ya dace su zamo masu yanke hukuncin karshe, a kan gudanar ayyukan tallafi da MDD ke samarwa.

Har ila yau jami'in na Sin ya bayyana bukatar sanya hukumomin kasashen da ake gudanar da irin wadannan ayyuka, cikin tsarin zabar jami'an da za su rika taimakawa ayyukan, bisa sassan da kasashen ke ganin akwai bukatar baiwa fifiko.

Ma ya kara da cewa, ya dace a aiwatar da gyare gyaren da aka yiwa kudurorin shirin samar da ci gaba na MDDr, ta yadda hakan zai tabbatar kasashen da za su amfana, na da cikakken ikon cin gajiyar sa, da ma tabbatar da nasarar ajandar ci gaban su ta nan da shekarar 2030.

Har ila yau ya ce, ya dace a ci gaba da martaba tsarin ci gaban da kasashen suka zabawa kan su, musamman ma kasashe masu tasowa, gwargwadon yanayin da suke ciki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China