in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakan Sin na samar da al'umma mai kyakkyawar makoma za su shafi tsaron intanet, in ji jami'in Sin
2017-12-20 09:45:17 cri

Jami'in tsare-tsaren harkokin tsaron Intanet na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Long Zhou ya bayyana cewa, matakan da kasar Sin ta ke dauka na bunkasa sabuwar alakar hadin gwiwar kasa da kasa da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil-Adama, za su shafi batun tsaron intanet.

Mr Long Zhou wanda ya bayyana hakan yayin wani taron dandalin tattaunawa game da tsaron intanet karo na 12 da ya gudana a birnin Geneva, ya ce daukacin masu ruwa da tsaki da masu amfani da intanet na da wannan buri, don haka, hanya daya kacal ta magance matsalar da harkar tsaron Intanet ke fuskanta ita ce ta yin hadin gwiwa.

Ya ce, a shirye kasar Sin ta ke ta yi aiki da dukkan bangarorin da abin ya shafa, domin ganin an kula da harkokin intanet kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada cikin lumana ba tare da wata rufa-rufa ba.

Jami'in na kasar Sin ya ce, muddin ana bukatar kwalliya ta biya kudin sabulu a fannin tsaron intanet, kamata ya yi kasashen duniya su rika martaba ka'idojin zaman lafiya da hadin gwiwa, a wani mataki na bullo da sabbin tunanin hadin gwiwa da daidaito da samar da dauwamamman tsaro.

A cewarsa, muddin ana fatan bunkasa tsaron intanet, akwai bukatar kasashen duniya su fito da managartan dokoki, wadanda za su kasance karkashin jagorancin MDD.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China