Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya bukaci al'ummomin kasashen duniya su taimaka wajen ciyar da tsarin siyasar jamhuriyar demokradiyyar Congo DRC gaba.
Wu Haitao, ya bayyanawa kwamitin sulhu na MDD a jiya cewa, ya kamata kasashen duniya su ci gaba da aiki don ganin bangarori daban daban na kasar sun cimma maslaha a siyasance ta hanyar tuntuba da tattaunawa, tare da mara baya ga shiga tsakani da kungiyoyin yankin kamar AU da kungiyar raya yankin babban tafki ke yi.
Ya kara da bukatar kasashen duniya su tabbatar da shugabancin gwamnatin kasar wajen warware rikicin, tare da martaba ikon kasar na mallakar yankunanta.
Wu Haitao, ya ce gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar Congo ce ke da nauyin kare fararen hula, kuma abun da ya kamata kasashen waje su yi shi ne, taimakawa gwamnatin inganta harkokin tsaro.
Ya ce, har kullum kasar Sin na taimakawa tsarin wanzar da zaman lafiya, tare da shiga harkokin wanzar da zaman lafiya a kasar, har ila yau, ya ce kasar Sin tana ba ta tallafin kayayyakin agaji, kuma tana ba da gudunmuwa wajen inganta zamantakewa da tattalin arzikin kasar. (Fa'iza Mustapha)