in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UN: Sin na daf da kawar da cutar zazzabin cizon sauro
2018-05-23 10:28:32 cri

Mataimakiyar ministan hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Cui Li, ta ce kasar Sin na daf da kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro ko malaria tsakanin al'ummar ta, matakin da ya samu yabo daga hukumar lafiya ta duniya.

Cui Li, ta bayyana hakan ne ga mahalarta wani taro na musamman a jiya Talata, a gefen taron shekara shekara na dandalin kasa da kasa game da harkokin kiwon lafiyar al'umma wanda ya gudana a birnin Geneva.

Cui Li, ta jagoranci taron da aka yiwa lakabi da "kasashen dake sahun gaba, da kokarin kasashe daban daban wajen yaki da cutar ta malaria domin cimma nasarar inganta kiwon lafiyar daukacin al'umma " Inda ta bayyana cewa, a shekara ta 2017, a karon farko ba a samu wani daga cikin kasar ta Sin da ya kamu da cutar Malaria ba, wanda hakan muhimmin mataki ne, a kokarin da ake yi na ganin bayan cutar baki daya.

Tuni dai mahukuntan kasar suka ayyana shekarar 2020, a matsayin lokacin da ake hasashen kauda cutar zazzabin cizon sauro baki daya daga daukacin yankunan Sin.

Da take tsokaci game da hakan, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yabawa Sin, bisa daukar nauyi da ta yi da hadin gwiwar Myanmar da Sri Lanka, na samar da kudaden da ake bukata don yaki da malaria.

Tedros ya ce, tun daga shekara ta 2000 kawo yanzu, an samu sakamako mai gamsarwa a wannan fanni, kuma an kai ga wata muhimmiyar gaba, sai dai duk da haka, ya zama wajibi a kara kaimi wajen tabbatar da dorewar hakan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China