in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya gabatar da sakon fatan alheri gabanin bikin ranar yara ta kasa da kasa
2018-05-31 19:18:01 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon taya murna ga yara 'yan kasar Sin, yayin da ake daf da fara shagulgulan ranar yara ta kasa da kasa. Shugaban na Sin ya bayyana fatan alherin ne, cikin wata wasika da ya aike ga yaran wata makarantar firamare a jiya Laraba.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana kuma shugaban kwamitin koli na hukumar zartaswar rundunar sojin kasar Sin, ya yi fatan daliban za su kara azama, wajen koyi daga tarihin juyin juya hali, da ci gaba da kuma sauye sauye da kasar Sin ta samu.

Ya ce, yana fatan yaran za su yi koyi daga kyawawan misalai na 'yan mazan jiya, wadanda suka sadaukar da rayuwar su domin gina JKS, da kasar Sin, da ma al'ummarta, da kyawawan al'adun kasa.

Shugaba Xi, ya ce yana fatan ganin daliban sun martaba ingantacciyar rayuwa da suka samu, su yi kyakkyawan amfani da lokacin rayuwar su, su dage da neman ilimi, su yi aiki tukuru wajen ba da ta su gudummawar ginin kasa, da raya al'ummar su da ma rayuwar 'yan baya.

Sakon dai na shugaba Xi, ya biyo bayan wata wasika da 'yan makarantar firamare ta Zhaojin dake lardin Shaanxi su 51 suka rubutawa shugaban na Sin, bayan da ya ziyarci makarantar a watan Fabarairun shekarar 2015. Garin Zhaojin dai ya taba kasancewa sansani na dakarun juyin juya hali na kasar Sin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China