in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya gana da yariman Birtaniya Andrew
2018-05-29 19:34:14 cri

A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da yariman Birtaniya mai rike da mukamin "duke of York" Andrew Albert Christian Edward a nan birnin Beijing. Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa manufar bude kofa ga kasashen waje, domin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a sabbin fannoni.

Ya ce idan an nuna kwazo da himma kan hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha tsakanin Sin da Birtaniya, ko shakka babu sassan biyu za su ci gajiya, tare kuma da samun moriyar juna, matakin zai kuma sa kaimi ga ci gaban huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin tana son kara zurfafa cudanya tsakanin manyan jami'anta da na Birtaniya, domin ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba yadda ya kamata.

A nasa bangare, yarima Andrew ya bayyana cewa, kasarsa tana maida hankali sosai kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, tana kuma fatan za a kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a fannonin kimiyya da fasaha, da kirkire-kirkire, da samar da kayayyaki da sauransu, kana tana fatan za a yi kokarin kara fahimtar juna dake tsakanin al'ummun kasashen biyu, ta yadda za a ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba cikin lumana. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China