in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai jagoranci taron kolin SCO da zai gudana a Qingdao
2018-05-28 10:17:03 cri
Dan majalisar zartaswar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya sanar da cewa, shugaba Xi Jinping na kasar ta Sin zai jagoranci taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO karo na 18.

Wang wanda ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, ya ce, taron kolin zai gudana ne daga ranar 9 zuwa 10 ga watan Yunin a birnin Qingdao dake lardin Shandong na gabashin kasar Sin.

Shugabannin kasashe mambobin kungioyar da kasashe 'yan kallo da ma shugabannin kungiyoyin kasa da kasa masu ruwa da tsaki na daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron kolin.

Wang Yi ya bayyana cewa, wannan taro shi ne na farko da aka kira tun bayan da kungiyar ta SCO ta kara yawan mambobinta. Yayin wannan taro, bangarorin daban-daban za su ci gaba da nacewa ga tunanin SCO na amincewa da juna, samun moriya tare, daidaito, yin shawarwari da mutunta al'adu daban-daban, gami da samun bunkasuwa tare", kuma za su tattauna kan yadda za a zurfafa hadin gwiwa ta fuskar samun zaman lafiya da tsaro, da inganta hadin gwiwa a fannin tsare-tsare, da ciyar da hadin gwiwa tsakaninsu da sauran bangarori bisa sabon yanayin da ake ciki a halin yanzu. Haka kuma taron zai shata wani daftarin bunkasa SCO a dukkanin fannoni. Daga karshe kuma za a fitar da sanarwar Qingdao. (Ibrahim/Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China