in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya yi kira da a gina Sin wadda za ta zamo jagora a fannin kimiyya da fasaha
2018-05-28 19:08:10 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen tabbatar da kasar Sin ta zamo a sahun gaba wajen raya kimiyya da fasaha.

Xi Jinping wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, yana mai cewa, burin kasar sa shi ne zama mai wadata da walwala, don haka dole a kara maida hankali ga bunkasa fannonin kimiyya da fasaha, ta yadda za ta kasance ja gaba a fannin kere kere da binciken kimiyya a duniya.

Shugaba Xi ya yi wannan tsokaci ne cikin wata sanarwa da aka fitar, yayin bude taro na 19 na masana fannin kimiyyar kasar Sin, da taro na 14 na masana fannin injiniyanci na kasar.

Ya kuma kara da cewa, yanayin da ake ciki, da kalubalen da ake fuskanta, na da matukar muhimmanci, don haka akwai bukatar masu ruwa da tsaki a fannonin kimiyya da fasaha su yi amfani da wannan dama, su tunkari matsaloli, tare da shawo kan duk wani kalubale.

Ya ce, akwai bukatar masanan su yi duk mai yiwuwa, wajen tabbatar da sun ba da gudummawa, ta samar da ci gaban kasa ta hanyoyin kimiyya da fasaha, su kuma sauke nauyin dake wuyan su bisa tarihi, ta yadda za su zamo karfi da zai samar da kirkire-kirkire a sabon zamanin da ake ciki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China