in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Amurka da ta cika alkawarin da ta yi
2018-05-30 20:18:45 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, sanarwar da Amurka ta bayar kwanan baya, game da karbar harajin hajojin kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kasarta, ya sabawa matsayar da sassan biyu wato Sin da Amurka suka cimma a Washington, wanda hakan ka iya zubar da kimar kasar ta Amurka a duniya. Kaza lika idan har Amurkan ta ci gaba da nacewa kan hakan, kasar Sin za ta dauki mataki mai karfi domin kiyaye moriyarta.

Hua ta fadi hakan ne a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing.

An ce, fadar White House ta bayar da wata sanarwa jiya, inda ta bayyana cewa, za ta sanar da sunayen kayayyakin fasahohin masana'antun masu darajar dalar Amurka kusan biliyan 50, wadanda za ta shigar daga kasar Sin kafin ranar 15 ga watan Yunin dake tafe, kuma za ta kara karbar harajin kwastan na kaso 25 bisa dari kan wadannan hajoji.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China