Dan majalissar zartaswar kasar Sin Mr. Guo Shengkun, ya gana da ministan ma'aikatar lura da harkokin cikin gidan Afirka ta Kudu Malusi Gigaba a birnin Beijing na kasar Sin a jiya Alhamis.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin da suke tattaunawa, Mr. Guo ya bayyana cewa, Sin na da burin ganin ta hada kai da Afirka ta Kudu, wajen bunkasa hadin gwiwar sassan biyu, a matsayin wani mataki na tabbatar da aiwatar da manufofin da shuwagabannin kasashen suka amincewa.
Har wa yau jami'an biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi kiyaye takardun shaidar tafiye-tafiye, da na dakile ci rani ba bisa ka'ida ba, da kuma batun yadda za a kara daukar matakan kare martabar al'ummun kasashen juna.(Saminu)