Majalisar dokokin kasar Afrika ta Kudu, ta amince a jiya Talata, da tsarin karbe ikon filaye daga hannun wasu mutane ba tare da biyan diyya ba.
Sai dai a cewar kakakin jam'iyyar ANC dake majalisar Nonceba Mhlauli, dole ne a aiwatar da tsarin bisa tabbatar da wadatar abinci da habakar tattalin arziki da kuma sauya tsarin tattalin arzikin kasar tun daga tushe.
Bangaren adawa dai ya nuna kin amincewarsa da batun tilasta sayen fili, yana mai cewa, zai yi nakasu ga ayyukan yi tare da yin barazana ga wadatuwar abinci. (Fa'iza Mustapha)