in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Real Madrid ta lashe kofin zakarun nahiyar turai a karo na 3 a jere
2018-05-30 18:19:51 cri
Kungiyar wasan Real Madrid ta doke Liverpool da ci 3-1 a wasan karshe da suka buga a daren Asabar na kofin zakarun turai na 2018 UEFA, kungiyar wasan ta samu nasarar daukar kofin a karon farko sau 3 a jere bayan kungiyar wasan Bayern Munich data samu irin wannan nasarar a shekarar 1976.

A wasan da aka buga a filin wasan NSC Olympic stadium a gaban 'yan kallo sama da 63,000, dukkannin kungiyoyin wasan biyu sun taka rawar gani a farko fara wasan.

To sai dai, raunukan da Mohamed Salah ya samu da kuma maye gurbinsa da Dani Carvajal ya rage armashin wasan tun a zagayen farko na wasan, wanda aka tashi ba tare da zara koda kwallo guda ba daga bangarorin biyu.

Zinedine Zidane shine ya kwace ikon sarrafa kwallon a 'yan sa'oi kadan da fara wasan a zagaye na biyu, yayin da Karim Benzema ya sanya su gaba mintoci 51 bayan fara wasan.

Sadio Mane ya shirya zara kwallon bayan wasu mintoci 4, amma a cikin mintoci 64 da fara wasan Gareth Bale ya zarawa Real Madrid kwallo ta biyu.

Bale ya zara kwallonsa ta biyu a mintoci 83 da fara wasan, inda hakan ya baiwa kungiyar wasan nasara a fafatawar da aka yi.

Wannan nasarar, ta baiwa Real Madrid nasarar zama zakara a wasan zakarun turai karo na 13, inda ta samu matsayin kungiyar wasan data fi kowacce samun nasara a tarihin gasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China