Kenya ce zata karbi bakuncin wasan da zasu buga da abokiyar takararta ta yammacin Afrika a Machakos a ranar 6 ga watan Yuni, kana bayan dawowarsu da mako guda kuma su fafata a Malabo. Kungiyar wasan da ta yi nasara ce zata samu tikitin shiga gasar kofin kasashen na Afrika karo na 11, wanda za'a gudanar tsakanin 27 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba a kasar Ghana.
Ouma ya bayyana cewa 'yan matan da zasu taka ledar sun nuna kwazo suna fatar halartar gasar ta Ghana. Za'a gudanar da shirin samun horon cikin nasara da kwarin gwiwa, kuma suna sa rana samun galaba akan abokan karawar tasu a wasan farko da zasu buga a Machakos.
Kenya ta doke Uganda a wasan farko da ci 1-0, wannan ya kara musu kwarin gwiwa inda suke fatan yin galaba akan Equatorial Guinea.
Kociyan yace, irin sabbin dabarun da 'yan wasan mata ke nunawa abun alfahari ne. Yace zasu canza sabon salo, kuma sabbin 'yan wasan da aka zaba suna nuna sha'awarsu wajen koya da kuma yin wasa yadda ya kamata. Yace zasu duba hanyoyin da zasu tsare gidansu daga abokan karawarsu.
Ouma ya jaddada bukatar 'yan wasan su zauna cikin shiri sakamakon jan aikin dake gabansu a wasannin biyu da zasu buga a Malabo.
"Hakika muna son lallasasu kuma sirrin dake tattare da hakan shine zamu bisu har gida mu lallasasu, kuma zasu tabbatar bamu mika musu wuya ba. Amma dole ne sai mun tsaya tsayin daka. Amma zamu jira har sai mun isa Malabo. Amma yanzu abinda da muke bukata shine mu fara yin galaba a wasan da zamu buga dasu a cikin gidab tukuna", inji kociyan.
Equatorial Guinea, kamar dai kasar ta Kenya, ta taba yin nasara, a wasan share fagen gasar cin kofin mata na Afrika a shekarar 2016 a jamhuriyar Kamaru kuma tana son samun wannan matsayi a karo na 4.
Kenya ta shirya taka leda a wasan kofin kwararru na Afrika na mata wato CECAFA a Kigali, na kasar Rwanda, sai dai an soke wasan sakamakon karancin kudade yayin da ya rage sa'oi 11 a gudanar da wasan. Sai dai Ouma yace ba zasu sauya matsayinsu ba game da shiryr shiryen.(Ahmad Fagam)