in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya ce Sin aminiyar kasarsa ce abun dogaro
2018-05-29 20:15:26 cri

Yayin taron ganawa da manema labarai da aka saba yi a nan birnin Beijing, a yau Talata kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasarta tana fatan yin hadin gwiwa cikin dogon lokaci bisa manyan tsare-tsare da kasar ta Rasha, domin samun moriyar juna.

An ce, a kwanakin baya bayan nan, shugaban kasar Rasha Putin, ya bayyanawa mahalarta dandalin tattalin arzikin kasa da kasa da aka shirya a birnin Saint Peterburg na kasarsa cewa, kasar Sin aminiyar Rasha ce kuma abar dogaro. Ya ce kudurori daban daban da aka tsayar yayin babban taron JKS karo na 19, sun samar da sharudda masu inganci, wajen kara zurfafa huldar dake tsakanin Sin da Rasha. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China