in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya gana da mataimakin shugaban Sin
2018-05-25 10:42:43 cri

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gana da mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan a jiya Alhamis, kuma sun cimma matsaya game da zurfafa dangantaka da hadin gwiwa domin amfanin al'ummomin kasashen biyu, da ma duniya baki daya.

A yayin ganawar tasu, Wang ya nuna cewa, cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Rasha tana da matukar alfanu, ba wai ga kasashen biyu ba, har ma ga duniya baki daya.

Mataimakin shugaban kasar ta Sin ya jaddada cewa, a bisa ga tarihin dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, ayyukan ci gaban da ake samu karkashin hadin gwiwarsu yana dacewa da muradun kasashen biyu a zahiri.

A nasa bangaren Putin ya ce, dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin tana kara ci gaba zuwa matsayin koli, ya kara da cewa, mu'amalarsu ta fannin siyasa tana kara zurfafa, dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen tana kara bunkasuwa, mu'amalar ciniki da tattalin arziki tsakanin kasashen tana kara samun tagomashi, dangantakar kasashen ta bangaren manyan ayyukan yana gudana cikin sauri, kana mu'amala tsakanin mutum da mutum a yankunan kasashen biyu yana kara samun kyautatuwa.

Ya kara da cewa, a nata bangaren kasar Rasha a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin don kara zurfafa dangantakar dake tsakaninsu daga dukkan fannoni, da nufin kara samun fahimtar juna da taimakekeniya kan harkokin kasa da kasa, da kuma ci gaba da tallafawa juna don daga martabar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa matsayin koli.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China