in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Rasha sun amince za su karfafa hadin gwiwa
2017-11-02 09:58:48 cri

Kasashen Sin da Rasha sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi kimanin 20, cikinsu har da batun zuba jari, makamashi da kuma binciken sararin samaniya.

An cimma wannan matsaya ne bayan kammala taron shugabannin gwamnatocin kasashen biyu wanda aka saba gudanarwa a karo na 22, wanda aka gudanar da shi a babban dakin taron dake Beijing.

A lokacin ganawar, firaiministan kasar Sin Li Keqiang, ya fadawa takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvedev cewa, a matsayinsu na makwabta na kusa, Sin da Rasha sun samu gagarumin ci gaba ta fuskar tsara ingantaccen shirin karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.

Li ya kara da cewa, kasar Sin ita ce babbar kasa mai tasowa a fadin duniya, kana ci gaba shi ne babbar hanyar warware dukkan matsaloli.

Dukkanin kasashen biyu suna daukar ci gaban junansu da muhimmanci a matsayin wata babbar dama ce, don haka akwai kyakkyawar makoma ga kasashen biyu ta yadda zasu hada kai da junansu domin samar da wani muhimmin tsarin da zai tabbatar da ci gaban kasashen a dukkan fannoni.

Medvedev, shi ne shugaban gwamnati na farko da ya ziyarci kasar Sin tun bayan da kasar ta kammala babban taronta na wakilan jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar karo na 19, kana ya taya kasar Sin murnar nasarar kammala taron na JKS cikin nasara, sannan yana fata za'a cimma nasarori da aka sanya gaba.

Ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta kai babban matsayi a tarihi, inda ake samun muhimman ziyarorin juna a tsakanin bangarorin biyu, da kyakkyawar hadin gwiwa a wasu manyan tsare tsare da bunkasuwar harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakaninsu.

Ya ce, kasar Rasha tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin makamashi, gina ababen more rayuwa, sufurin jiragen sama, da kuma fadada sabbin hanyoyi da suka hada da kasuwanci ta yanar gizo da hada hadar kudade da zuba jari, da kuma karfafa musayar raya al'adun gargajiya tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

Bayan kammmala taron, Li da Medvedev, sun rattaba hannu kan sanarwa bayan taron wanda aka rabawa manema labarai.

Da yammacin ranar Laraba, Li da Medvedev, suka halarci bikin kammala taron musayar harkokin watsa labarai tsakanin kasar Sin da Rasha na wannan shekara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China