in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an kasashen Sin da Amurka sun gana da juna
2018-05-24 10:43:41 cri
A jiya Laraba, bisa agogon kasar Amurka, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, lokacin da jami'in kasar Sin ya tsaya a birnin Washington na kasar Amurka, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida, bayan da ya kammala wata ziyarar a kasar Argentina.

Yayin ganawarsu, Wang Yi ya ce, a yanzu haka yanayin da kasashen duniya ke ciki na da sarkakiya, saboda haka kokarin kiyaye hulda mai kyau tsakanin Sin da Amurka na da muhimmanci sosai. Don cimma wannan burin, matakan da za a dauka sun hada da:

Na farko, bari shugabannin kasashen 2 su tabbatar da manyan tsare-tsaren da za a yi amfani da su, wajen raya hulda tsakanin kasashen Sin da Amurka. Na biyu, a yi kokarin zurfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin bangarorin 2, don tabbatar da tushen huldar dake tsakaninsu. Na uku, habaka hadin kan Sin da Amurka a fannin harkokin yankin da ake ciki da na kasa da kasa.

A nasa bangare, mista Mike Pompeo ya ce, a ganin kasar Amurka, huldar dake tsakaninta da kasar Sin, ba wai wani bangare daya ne ke samun riba ba, ta yadda wani bangare na daban tilas ya yi hassara. Saboda haka kasar na son yin kokari tare da kasar Sin, don kara kyautata huldar dake tsakaninsu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China