in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya dandalin kasa da kasa don yaki da ta'addanci a Beijing
2018-05-28 21:01:33 cri

Yau Litinin ne aka kaddamar da taron dandalin kasa da kasa na yaki da ta'addanci mai taken "Babbar ganuwa-shekarar 2018", a kwalejin horas da 'yan sanda na musamman. Za kuma a shafe kwanaki 4 ana gudanar da dandalin.

Wakilai sama da 180 da suka zo daga kasashe 28, ciki har da kasar Sin da Faransa da Pakistan da Jordan da Masar da Mexico, sun halarci bikin bude dandalin. Babban taken dandalin shi ne yaki da ta'addanci a tuddai, kuma mahalarta dandalin za su yi tattaunawa kan batutuwan dake shafar ayyukan ba da jaroganci, da leken asiri da dai sauransu.

Yayin bikin, mataimakin kwamandan rundunar 'yan sandan kasar Sin Qin Tianzhong ya bayyana cewa, makasudin shirya dandalin shi ne, kara karfafa hadin gwiwar tsakanin kasa da kasa wajen tunkarar ta'addanci, tare kuma da kiyaye kwanciyar hankali da zaman karko a fadin duniya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China