in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci kwamitin tsaronta ya taimaka wajen yakar ta'addanci a yammacin Afrika da Sahel
2017-07-14 14:58:21 cri

Jakadan MDD game da batun Afrika ya bukaci kwamitin tsaron MDDr da ya kara tallafawa yaki da ta'addanci a yammacin Afrika, ciki har da karfafa ayyukan kwamitin a yankin Sahel.

Shugaban ofishin MDD mai kula da al'amurran Afrika (UNOWAS) Mohamed Ibn Chambas, ya bayyana ta'addanci da tsattsauran ra'ayin addini da cewa suna yin sanadiyyar jefa al'umma cikin matsalar tashe tashen hankula da kuma illata 'yancin mallaka na yankunan, ya ce kasashen da suka fi fama da barazanar sun hada da yammacin Afrika da yankin Sahel, wanda ya hada da kasashen Mali, Mauritania, Kamaru, Burkina Faso, Senegal, Nigeria, Niger da Chad.

Kokarin yankunan kasashen zai bunkasa ci gaba wajen tabbatar da samun karuwar zuba jari, da inganta kayayyakin more rayuwa da samar da guraben aikin yi.

A yankin Sahel, ana ci gaba da fuskantar tashin hankali a Mali, inda ya watsu zuwa kasar Burkina Faso da yammacin jamhuriyar Nijer.

Jami'in MDD ya bukaci kwamitin tsaron MDD ya dauki karin matakan kara azama wajen yaki da ta'addancin da kuma tsattsauran ra'ayin addini.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China