in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da karfafa karfin yaki da ta'addanci na kasashen Afrika
2016-12-06 10:32:34 cri

Shugaban kasar Senegal Macky Sall da Herve Ladsous, mataimakin sakatare janar kan ayyukan tabbatar da zaman lafiya na MDD, sun yi kira a ranar Litinin a birnin Dakar ga karfafa karfin mayar da martani na sojoji da jami'an tsaro na kasashen Afrika domin fuskantar barazanar ta'addanci.

Da suke magana a yayin bude taro karo na uku na dandalin kasa da kasa na Dakar kan zaman lafiya da tsaro a Afrika, shugaba Sall ya jaddada cewa, ya zama wajibi da a karfafa karfin mayar da martani na sojoji da jami'an tsaro gaban wannan barazana ta ko ina, musamman ma wanda ke da nasaba da ta'addanci.

A cewarsa, a yawancin kasashen Afrika, rundunonin sojojin kasashen ba su shirya ba. Ba laifin sojoji ba ne. Afrika ta fuskanci wani lokaci na tsarin gyaran kasa, dake hana samar da kayayyaki a wannan fanni, in ji shugaba Macky Sall.

A wannan lokaci, ya kamata kasashen Afrika su yi kokarin cikin gida da farko domin sake maida sojoji da jami'an tsaro bisa matsayinsu, samar musu da kayayyaki da kuma mutane, da kuma samar musu da horo, a cewar shugaban Senegal tare da jaddada cewa, domin yaki da 'yan ta'adda, dole sojoji da jami'an tsaron kasashen Afrika su sami horo da kayayyakin aiki.

A nasa bangare, mista Herbe Ladsous ya shawarta karfafa karfi da zamanintar da tsare tsaren tsaron kasashe, tare da jaddada cewa, MDD tana da babbar kwarewa da ya kamata ta bayar ga kasashen dake bukata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China