in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na shirin kafa sabon ofishin da zai yaki ayyukan ta'addanci
2017-02-23 10:36:02 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya gabatar da kudurin kafa wani sabon ofishin da zai jagoranci kokarin majalisar na yaki da ayyukan ta'addanci a duniya.

Guterres ya shaidawa zauren majalisar yayin wani taro a jiya cewa, ofishin zai kasance karkashin sabon karamin sakatare janar, kuma zai kunshi jami'an majalisar da ke aikin yaki da ta'addanci.

Ya ce, za a dorawa ofishin nauyin aiwatar da manufofin MDD na yaki da ayyukan ta'addanci, tare da taimakawa kasashen mambobin majalisar yakar mummunar ta'addar.

Guterres ya ce, manufar ita ce, hada hannu da kasashe mambobin MDD wajen yaki da barazanar ta'addanci dake bukatar daukin gaggawa.

Har ila yau, ya ce aikin sabon ofishin, zai kasasnce karkashin goyon baya ko bukatar kasasehe mambobin MDD. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China