in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka tana son yin shawarwari da Sin kan batun kudin kwastan, in ji WTO
2018-04-19 13:12:59 cri
Bisa bayanin da kungiyar ciniki ta duniya wato WTO ta fidda, an ce, kwanan baya, kasar Amurka ta nuna fatanta ga kungiyar cewa, tana son yin shawarwari da kasar Sin kan batun kara kudin kwastan bisa sashe na 232 na dokar cinikin kasarta na shigowar kayayyakin karfe da samholo da kuma bincike bisa sashe na 301 na dokarta, a karkashin tsarin warware sabani na kungiyar WTO. Hakan ya dace da ka'idar WTO wajen warware sabanin ciniki a tsakanin kasa da kasa.

Cikin bayanin, WTO ta kuma bayyana cewa, ko da kasar Amurka ba ta yarda da bukatun da kasar Sin ta gabatarwa kungiyar ba, amma, tana son yin shawarwari kan batutuwan.

Dangane da matakin da kasar Amurka ta dauka bisa sashe na 232 na dokarta wajen kara haraji kan kayayyakin karfe da samholo da ta shigo da su daga ketare, kasar Amurka ta bayyana cewa, an dauki matakin ne ba domin kariyar ciniki ba, sai hana shigowar kayayyakin karfe da samholo wadanda suka kawo barazana ga tsaron kasar ta Amurka. Haka kuma, tana ganin cewa, tsarin WTO wajen warware sabanin ciniki a tsakanin kasa da kasa, ba zai taimaka wajen warware matsalar kudin kwastan dake shafar tsaron wata kasa ba.

Amma, kasar Amurka ta bayyana cewa, tana son yin shawarwari kan batutuwan dake shafar bincike kan sashe na 301 na dokarta da ta yiwa kasar Sin, amma ya zuwa yanzu, ba a fara aiwatar da matakan kara harajin a hukumance ba, shi ya sa, babu bukatar a warware matsalolin da kasar Sin ta gabatarwa kungiyar, bisa tsarinta na warware sabanin ciniki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China