in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaiministan Sin ya ce kasashen Sin da Amurka ba za su shiga yakin ciniki ba
2018-05-20 11:26:04 cri
Wakilin musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasar Sin Liu He ya bayyana a jiya Asabar cewa, kasar Sin da Amurka sun cimma matsaya game da batutuwan da suka shafi ciniki da tattalin arziki, inda suka yiwa juna alkawarin ba zasu shiga yakin ciniki a tsakaninsu ba.

Liu wanda ya isa birnin Washington da yammacin ranar Talata domin tuntubar bangaren Amurka game da batun ciniki da tattalin arziki a wani goron gayyatar da gwamnatin Amurkar ta gabatarwa gwamnatin Sin.

A zantawarsa da kafafen yada labarai a ranar Asabar, Liu ya bayyana cewa, bangarorin biyu sun cimma matsaya ba zasu kaddamar da yakin ciniki ba, kuma zasu dakatar da batun tsawwala kudaden haraji ga junansu, wanda shi ne babban batun da aka fi mayar da hankali a yayin tattaunawar tasu.

Ya bayyana cewa, ziyararsa zuwa Amurkar ta samar da kyakkyawan sakamako, ta bada ma'ana, kuma ta haifar da gamsasshen sakamako, Liu ya kara da cewa, babban dalilin da ya haifar da samun wannan nasara shi ne, matsayar da aka cimma tsakanin shugaba Xi da takwaransa na Amurka Donald Trump a kwanakin baya, kuma babban abin dubawa shi ne bukatun al'ummomin kasashen biyu da ma duniya baki daya.

Liu ya ce, bangarorin biyu zasu karfafa dangantakarsu a bangarorin da suka hada da makamashi, kayan amfanin gona, kiwon lafiya, kayayyakin fasahar zamani da kuma harkokin kudi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China