in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya za ta kara inganta ayyukan tattara bayanan sirri
2018-03-07 10:47:02 cri
Shugban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa na mayar da hankali kan bunkasa karfin kasar na tattara bayanan sirri domin fatattakar ta'addanci da sauran laifuka.

Muhammadu Buhari ya ce domin cimma wannan manufa, dole ne a san cewa aikin tattara bayanan sirri, ba aiki ne da ya dogara kacokan a kan hukumomin tsaro ba.

Shugaban ya bayyana haka ne a Abuja, yayin taro kan tsaron kasa karo na 8, da kungiyar tsoffin daliban kwalejin tsaron kasar ta shirya, a daidai lokacin da kasar ke juyayin rahotanni sace 'yan matan sakadare 110 da kungiyar Boko Haram ta yi a ranar 19 ga watan Fabreru.

Muhammadu Buhari ya ce dole ne aikin ya kunshi kowane dan kasar da kowacce al'umma. Sannan dole ne musayar bayanan sirri ya zama doka a tsakanin hukumomin soji da na tattara bayanan sirri.

Ya ce la'akari da yadda 'yan ta'adda da sauran bata gari ke amfani da kafar intanet da fasahar zamani, wajibi ne fasahar zamani ta zama babban abun da hukumomin tsaro za dauka da muhimmanci a fagen daga. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China