A jawabinsa na rufe taron, shugaban taron na MSC Wolfgang Ischinger, ya ce yana fatan za a cimma manufar shirya wannan taro, duk da cewa a jawabinsa na budewa ya nuna shakkun yin hakan.
Cikin abubuwan da aka tabo yayin taron na kwanaki uku, sun hada da rikicin yankin gabas ta tsakiya, da batun nukiliyar zirin Koriya da kawancen siyasa, tattalin arziki, al'adu tsakanin kasashen dake yankin tekun atilantika, da kokarin kungiyar EU na zurfafa alakar tsaro. Sauran sun hada da ra'ayoyi da hangen nesa da shawarwarin da aka yi musaya, kamar shawarar "Ziri daya da Hanya daya" da kasar Sin ta kirkiro da sabuwar yarjejeniyar tsaro da aka cimma tsakanin kungiyar EU da kasar Burtaniya bayan ficewarta daga kungiyar EU.
Sama da mahalarta 500 ne suka halarci taron, ciki har da babban sakataren MDD Antonio Guterres da sakataren tsaron Amurka James Mattis da ministan tsaron kasar Rasha Sergey Lavrov, da firaministar kasar Burtaniya Theresa May da babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Janar Jens Stoltenberg.(Ibrahim)