in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malariya ta gigita Mozambique a shekarar 2015
2016-01-11 10:18:29 cri

Kafafen yada labarai a kasar Mozambique sun rawaito a Lahadin nan cewar, lardin Tete dake shiyyar arewa maso yammacin kasar, shi ne yankin da ya fi fuskantar matsalar cutar zazzabin cizon sauro a duk fadin kasar, inda cutar ta hallaka mutane kimanin 213 a cikin shekarar 2015, adadin da ya zarta na shekarar 2014, inda mutane 22 suka rasu a sakamakon cutar.

A cewar kamfanin dillancin labaran kasar AIM, kimanin mutane dubu 370 ne suka ziyarci asibitoci a yankin na Tete don a sanadiyyar cutar ta zazzabin malariya a shekarar ta 2015, wanda shi ne adadi mafi yawa da aka taba fuskanta a kasar.

A shekarar 2014, mutane dubu 20 ne suka ziyarci asibitocin lardin na Tete, don shan magungunan cutar, daga cikin adadin mutane 22 suka rasu.

Shugaban cibiyar lafiyar kasar Regina Nassiaca, ya danganta karuwar hasarar rayukan da aka samu a shekarar ta 2015 da cewar, sakamakon rashin zuwan marasa lafiyan asibotocin yankin a kan lokaci, har sai da cutar ta ci karfin su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China