Jami'in wanda ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, fadar mulkin Najeriya, gabanin ranar yaki da zazzabin cizon sauro na duniya da aka saba gudanarwa ranar 25 ga watan Afrilun kowace shekara, ya ce muddin ana bukatar kawar da cutar baki daya, kamata ya yi gwamnati da al'umma baki daya su hada kai domin tsaftace muhallinsu maimakon su dogara ga maganin cutar kadai.
Mr Okechukwu ya kara da cewa, wajibi ne a fara tsaftace muhalli, wadda ke zama matattarar sauro, a matsayin matakin farko na kawar da cutar ta Malaria. Ya ce idan har aka samu nasarar yin haka,kusan za a magance kashi 50 cikin 100 na cutar.
Ya ce,ko da ya ke samar da kudaden yana da muhimmanci a kokarin ganin bayan wannan cuta,amma babu wata nasarar da za a cimma ko da an samar da biliyoyin dalaloli a tsarin kiwon lafiya, idan jama'a ba su tsaftace muhallinsu ba.
Taken ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro na bana da hukumar lafiya ta duniya ta ayyana, shi ne kawo karshen cutar ta malaria kwata-kwata. (Ibrahim)