in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Za a zabi 'yan wasan scrabble domin halartar gasar kasa da kasa
2018-05-23 09:30:54 cri

Babban kocin hukumar dake lura da 'yan wasan Najeriya masu wasan dara ta scrabble Anthony Ikolo, ya ce yanzu haka an fara gudanar da wasan kasa tsakanin 'yan wasan dake sassan Najeriya daban daban, domin zabar wadanda za su wakilci kasar a wasan na scrabble na duniya.

An bude wasan fidda zakarun ne na kwanaki 5 a birnin Fatakwal dake kudancin Najeriya tun daga ranar Litinin, inda ake fatan kammalawa a Juma'ar karshen makon nan. Ana kuma fatan zabar 'yan wasa mafiya kwarewa cikin mutane 20 dake halartar wasannin fidda gwanin na yanzu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China