in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kaddamar da gagarumin shiri na kawar da Boko Haram
2018-05-16 09:26:56 cri

A jiya Talata ne sojojin kasa na Najeriya suka kaddamar da wani gagarumin shiri na tsawon watanni hudu da nufin ganin bayan kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram a yankin tafkin Chadi.

Babban hafsan mayakan kasa na Najeriya Tukur Buratai, wanda ya sanar da hakan, ya ce manufar sabon shirin, mai suna, "Operation Last Hold" ita ce tabbatar da ganin an lalata dukkan tunga da wuraren da mayakan ke boye a kewayen yankin tafkin Chadi.

A cewar babban hafsan, shirin zai kuma taimaka wajen share hanyoyin ruwan tafkin, da ma abubuwan dake kawo cikas ga zirga-zirgar mutane da kwale-kwale a hanyoyin ruwan da suka kewaye tafkin.

Bugu da kari, sabon shirin zai tabbatar da ganin bayan sansanoni da tungayen mayakan na Boko Haram a yankin tafkin Chadin baki daya. Za kuma a kara kafa sabbin birget-birget da girke wasu muhimman kayan aiki na sojoji a jihar Borno.

A karshen sabon shirin, shi ne kawar da mayakan Boko Haram baki daya daga jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Mahukuntan Najeriya dai sun samu gagarumar galaba a kan mayakan na Boko Haram, inda suka fatattake su daga dajin Sambisa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China