in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta sa kaimi ga matasa wajen ci gaban kimiyya da fasaha
2018-05-16 10:43:50 cri

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, za ta sa kaimi ga matasa don bunkasa ci gaban kimiyya da fasaha da kuma kirkire kirkire.

Ministan kimiyya da fasaha na kasar Ogbonnaya Onu, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin wani 'dan Najeriya, Odedairo Oluwaferanmi Ayodele, wanda ya lashe lambar yabo ta zinari a gasar lissafi ta duniya wanda aka gudanar a kasar Thailand a kwanan nan, inda ya bayyana cewa, matasa su ne kashin bayan ci gaban kowace kasa a duniya.

Onu ya ce, dole za su baiwa matasa fiffiko saboda su ne kaso mafi yawa na al'ummar kasar.

Ya kara da cewa, ya zama tilas a yi amfani da su a fannonin kimiyya da fasaha saboda hakan zai taimakawa kasar wajen hana shigo da abubuwa masu yawa daga kasashen waje, ya kara da cewa, idan aka yi amfani da matasan a fannonin kimiyya da fasaha, za'a iya sarrafa kayayyakin da masana'antu ke amfani da su na cikin gida wadanda galibi a halin yanzu ake shigo da su daga kasashen waje.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China