in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta harba tauraron dan Adam mai aikin karba karba domin binciken barin wata mafi nisa
2018-05-21 09:01:40 cri

Kasar Sin ta cimma nasarar harba tauraron dan Adam mai aikin karba karba, domin binciken barin wata mafi nisa, a wani mataki na aiko da bayanai daga wannan yanki na wata zuwa doron duniya.

Da misalin karfe 5:28 na asubahin ranar Litinin ne aka harba tauraron mai lakabin Magpie Bridge, wanda zai yi aiki tare da tauraron Chang'e-4, an kuma harba tauraron ne da rokar Long March-4C, a tashar harba taurarin dan Adam dake Xichang.

Da yake karin haske game da wannan aiki, manaja mai kula da sabon tauraron da aka harba a hukumar kula da harkokin sama jannati ta kasar Sin ko CNSA a takaice Zhang Lihua, ya ce harba wannan tauraro, daya ne daga manyan matakan da kasar Sin ke dauka, game da burin ta na sauka, tare da samar da bayanai daga barin wata mafi nisa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China