in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta harba tauraron dan Adam na kasar Aljeriya
2017-12-11 09:27:55 cri

Kasar Sin ta gudanar da aikin harba tauraron dan Adama na sadarwa mallakar kasar Aljeriya, daga cibiyar harba tauraron dan Adama ta Xichang dake lardin Sichuan a kudu maso gabashin kasar ta Sin.

An dai harba tauraron ne mai lakabin Alcomsat-1 da sanyin safiyar ranar Litinin. Tauraron shi ne kuma irin sa na farko da kasar Aljeriya ta mallaka, wanda ya shaida hadin gwiwar kasashen biyu a fannin bunkasa fasahar sararin samaniya.

Aljeriya za ta yi amfani da wannan tauraron dan Adam wajen watsa shirye shiryen talabijin, da sadarwar gaggawa, da yada ilimi daga nesa, da inganta ayyukan hukuma ta kafofin zamani. Sauran sun hada da inganta sadarwa domin sana'o'i, da ci gaban masana'antu, da samar da hidimomin yanar gizo, da taswirar ban kasa da ake samarwa daga tauraron dan Adama.

Da misalin karfe daya saura minti ashirin na daren jiya ne aka harba tauraron na sadarwa da rokar Long March-3B, matakin da ya sanya wannan tauraron dan Adam kasancewa na 258, cikin jerin wadanda aka harba ta amfani da rokar Long March.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China