Hukumar kula da tsarin amfani da tauraron dan Adam ta kasar Sin, ta ce kasar za ta kaddamar da karin taurorin dan Adam na Beidou-3 a watan Nuwamban bana.
A cewar shugaban hukumar Ran Chenqgi yayin wani taron fasaha da ya gudana jiya, tsarin amfani da tauraron dan Adam wajen samar da bayanan kasa, zai gudanar da ayyuka ga kasashen dake cikin shirin 'ziri daya da hanya daya a cikin shekarar 2018, sannan zai fadada zuwa fadin duniya a 2020.
A halin yanzu, tsarin na iya samar da hidimomi ga yankuna Asiya da Pasifik.
Sin dai ita ce kasa ta 3 da ta samar da tsarin na amfani da tauraron dan Adam bayan Amurka da Rasha. (Fa'iza Mustapha)