in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kafa sabon kamfanin kera taurarin dan Adam a Wuhan
2018-04-27 09:54:31 cri

Yanzu haka shirye shirye sun yi nisa, game da kafa sabon kamfanin kera taurarin dan Adam a birnin Wuhan, fadar mulkin lardin Hubei dake tsakiyar kasar.

Kamfanin, a cewar shugaban sa Lyu Dongmin, zai maida hankali ga kera na'urorin sama jannati kanana, da sauran taurarin dan Adama na sayarwa. Kaza lika zai kunshi fannin bincike da samar da ci gaba a fannin kirar taurarin dan Adam. Haka kuma za a yi amfani da fasahohin zamani na sarrafa taurarin dan Adam yayin kirar sabbin na'urorin kamfanin.

A daya bangaren kuma, kamfanin zai yi hadin gwiwa da kamfanonin dake aiki a fannin sufurin sama jannati, wajen samar da damar kera sama da taurarin dan Adam 100 a duk shekara.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China