in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping da Peng Liyuan: Wannan ne yadda kauna take kasancewa
2018-05-20 17:45:24 cri

Kauna na nufin raka wa juna a duk tsawon rayuwa.

Bayan Xi Jinping ya zama shugaban kasa, kullum ya kan bayyana a gaban jama'a tare da uwargidansa Peng Liyuan. Inda su kan bayyanawa jama'a yadda suke dacewa da juna. Hakika sun riga sun kasance "Baba Xi" da "Mama Peng" a zukatan jama'a, sun kuma kasance abin koyi kan yadda miji da mata suke zama tare.

Zaman auren da ya fi sanya mutum jin dadi shi ne yadda iyalan wani suka karbi matarsa da hannu biyu-biyu. A lokacin bikin bazarar shekarar 2015, Xi Jinping ya koma kauyensa, ya gabatar da matarsa ga jama'ar wurin.

Abin da ya fi burgewa, shi ne, ko ina ka tafi, akwai wadda ta dauki hannunka. Sa'an nan lokacin da aka yi ruwan sama, za a daga laima dominka. A shekarar 2014, Xi Jinping ya yi rangadi a wani jirgin ruwa mai nazarin teku na kasar Sin. Lokacin da ya hau jirgin, ya juya jikinsa tare da mika hannunsa ga matarsa Peng Liyuan, ya ce, "Zo".

Jin dadin zaman aure, shi ne lokacin da aka zama an dace da juna. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da matarsa Peng Liyuan su kan sanya tufafi iri daya, don nuna kaunar dake tsakaninsu.


1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China