in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping da Peng Liyuan: Wannan ne yadda kauna take kasancewa
2018-05-20 17:45:24 cri

Kauna na nufin kulawa da juna.

Bayan aure, Xi Jinping ya kan kai ziyarar aiki a sauran wurare a matsayinsa na wani jami'in gwamnati. A nata bangare ma Peng Liyuan ta kan tafi sauran yankuna don nuna fasahar rera waka a matsayinta na wata shahararriyar mawakiya. Ko da yake da kyar suke iya zama tare, amma kullum suna nuna fahimtar juna da kulawa da juna. Yanayin wurin da Xi Jinping ke aiki na da sanyi, shi ya sa Peng Liyuan ta dinka masa wani babban bargo na zamani, a yayin da Peng Liyuan ke halartar manyan bukukuwan nuna fasahohi, Xi Jinping ya dafa mata dambu na Jiaozi , ya jira ta a gida.

Kauna na nufin kafa al'adar iyali ta gargajiya.

Suna bin al'adar iyali ta gargajiyar ta koyarwa diyarsu da'a, da sanya ta yin kokarin karatu da tsimin kudi. Sun baiwa diyarsu suna "Ze Ming", domin bayyana fatansu na ganin za ta kasance mai gaskiya bisa ma'anar sunan.


1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China