in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping da Peng Liyuan: Wannan ne yadda kauna take kasancewa
2018-05-20 17:45:24 cri

A nan kasar Sin, akwai wani sabon biki, wato yau ne ranar 20 ga watan Mayu. Saboda yadda ake karanta "520" da Sinanci ya yi yadda ake karanta kalmar "Ina son ki/ka" , hakan ya sa masu amfani da yanar gizo ta Internet na kasar Sin sun mayar da ranar a matsayin ranar musamman ta bayyana kauna. A wannan lokaci na musamman, an tuna da labarun kauna a tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Madam Peng Liyuan.

Xi Jinping yana mayar da hankali sosai kan nuna biyayya ga iyaye da kula da matarsa da diyarsa yadda ya kamata. Shi da matarsa Peng Liyuan suna nuna kaunar juna da goyon baya ga juna, daga "fara kaunar juna tun daga gamuwa da juna a karon farko" zuwa "zama tare har na tsawon duk rayuwa", sun kasance misalin yadda ya kamata miji da mata suke a zukatan jama'ar kasar Sin.

Kaunar dake tsakanin miji da mata na nufin idan ki/kana nan, to, za ku ji dadin zama.

A watan Satumban shekarar 1987, Xi Jinping ya yi aure da Peng Liyuan. Babu babban bikin aure,da ya wuce gayyaci wasu abokai da abokan aiki don cin abinci, har ma ana sayo alewar musamman don bikin aure ne cikin gaggawa. Amma, idan ana iya zama tare, to wannan shi ne jin dadin zaman aure .


1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China