Jakadar kasar Sin a Tanzania Wang Ke, ta shaidawa manema labarai a Dar es Salaam, yayin da ta kai ziyara ma'aikatar kudi da tsare-tsare na kasar cewa, ana samun nasara a tattaunawar da ake tsakanin gwamnatocin biyu kan aikin tashar Bagamoyo, inda ta ce aikin na da matukar muhimmanci ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Ta ce Gwamantocin Tanzania da Sin, sun tuntubi juna sosai game da aiki, inda ta ce ta na fatan za su cimma matsaya kan kwangilolin da suka shafi aikin don fara gudanar da shi nan bada dadewa ba, domin al'ummar Tanzania ta amfana.
An rattaba hannu kan matakin farko na yarjejeniyar gina tashar Bagamoyo ne tun a shekarar 2013, sai dai cimma yarjejeniyar karshe game da jarin gudanar da aikin na tafiyar hawainiya. (Fa'iza Mustapha)