Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen ketare, da kara azama wajen aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" yadda ya kamata, a kokarin ganin kasashen duniya sun ci gajiyar shawarar.
A ranar 15 ga wata, kasashen Sin da Trinidad da Tobago, suka daddale wasu bayanai, game da kara azama kan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". (Tasallah Yuan)