Babban mai tsara jirgin Huang Lingcai ya bayyana cewa, bayan da jirgin ya yi nasarar tashin gwaji a watan Disamban da ya gabata, an kuma shirya jirgin zai tashi daga cibiyarsa ta gudanar bincike dake Zhuhai zuwa Jingmen dake lardin Hubei a tsakiyar kasar Sin.
Daga nan ne kuma jirgin zai fara tashinsa na farko a cikin ruwa a makeken wurin adana ruwan nan dake Jingmen, wanda aka shirya a wani lokaci a wannan shekara, kamar yadda Huang kana babban injiniya a cibiyar binciken harkokin jiragen sama na hukumar AVIC ya sanar.(Ibrahim)