in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu a harin kauyen Gwaska dake Nijeriya ya karu zuwa 73
2018-05-09 11:01:40 cri

Adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar wani hari da aka kai kauyen jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Nijeriya, ya karu zuwa 73, inda a jiya Talata aka gano karin gawarwaki tare da binne su.

Galibin mazauna kauyen Gwaska mai yawan al'umma manoma ne. Kauyen mai nisan kilomita 291 daga birnin kaduna, ya kasance a yankin karamar hukumar Birnin Gwari, wanda ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga.

Mazauna kauyen sun yi ta gudun neman tsira, a lokacin da 'yan bindigar suka far musu da yammacin ranar Asabar, inda suka yi ta harbin kan mai uwa dawabi. Yara aka fi kashewa a harin da ya dauki tsawon sa'o'i 4.

An yi imanin cewa, maharan sun shigar kauyen ne daga jihar Zamfara, wadda ke makwabtaka da jihar ta Kaduna.

Mahara akalla 50 ne, suka shiga kauyen a kan babura, inda suka yi masa kawanya tare da kona gidaje, yawancinsu na laka.

Har ya zuwa jiya Talata, a lokacin da wakilin kamfanin Xinhua ya kai ziyara kauyen, wuta na ci gaba da cin wasu gidaje, yayin konanun babura da kekuna ke tarwatse a kauyen.

Kuma har zuwa lokacin, babu jami'an tsaro, duk da irin kisan da aka yi wa mazauna kauyen.

A wani yunkuri na cafke maharani ne, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana a ranar Asabar cewa, za ta tura jami'anta na yaki zuwa yankin Birnin Gwari. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China