in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane akalla 45 ne suka mutu sanadiyyar wani hari a Nijeriya
2018-05-07 09:20:17 cri

Mutane akalla 45 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu suka jikkata, yayin wani hari da aka kai kauyen Gwaska na jihar Kaduna dake arewa maso tsakiyar Nijeriya.

Wani ganau ya bayyana a jiya cewa, an kashe mutanen ne a ranar Asabar da rana, a lokacin da wasu tsageru suka farwa kauyen Gwaska dake yankin karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan an kashe wasu mutane 14 masu aikin hakar a yakin Janruwa na jihar.

Wani dan banga a yankin, Bala Abdullahi, ya ce tsagerun sun shiga kauyen Gwaska ne a kan babura ta hanyar jihar Zamfara, inda suka yi ta harbin kan mai uwa dawabi.

Da take tabbatar da al'amarin, gwamnatin jihar ta ce za a girke rundunar soji na din din din a yankin, domin dakile kashe-kashen da ake yi.

Gwamnan jihar Nadir El-Rufai, ya ce yana tattaunawa da gwamnatin tarayyar kasar game da lamarin, kuma ya umarci hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, ta kai wa wadanda harin ya rutsa da su agajin jin kai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China