in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya ta ce a shirye take ta karbe ikon tafiyar da harkokin tsaro daga hannun dakarun AU
2018-05-14 10:26:35 cri

Gwamnatin kasar Somaliya ta tabbatar wa kungiyar tarayyara Afrika AU da MDD cewa, a shirye take ta karbe harkokin tafiyar da al'amurran tsaron kasar daga hannun dakarun kiyaye zaman lafiya na AU kamar yadda aka tsara tun da farko.

Babban mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro, Abdisaid Musse Ali, ya fada wa taron hadin gwiwa na kungiyar AU da MDD dake sake fasalin tsarin wanzar da zaman lafiyar kasar cewa, ofishin shugaban kasar da gwamnatin kasar a shirye suke su karbe ikon tafiyar da harkokin tsaron kasar.

A wata sanarwa da tawagar wanzar da zaman lafiyar ta AU a Somaliya wato AMISOM ta fitar, ta ce, sauya fasalin shirin yana da matukar muhimmmanci wajen tsarawa da kuma tafiyar da harkokin tsaro a Somaliya.

A taron hadin gwiwar na AU da MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa da aka shirya a Mogadishu, sanarwa ta kara da cewa, shekaru masu yawa da suka shude, Somaliya tana ba da cikakken taimako da goyon baya ga tawagar wanzar da zaman lafiyar ta kasa da kasa wadda hakan ta baiwa kasar damar cimma gagarumar nasara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China