in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin bam ya yi sanadin mutuwar mutane 5 a Mogadishu
2018-03-26 10:08:54 cri

Mutane a kalla 5 sun mutu, wasu da dama kuma sun jikkata sanadiyyar fashewar bam cikin wata mota mai shake da boma bomai a birnin Mogadishu na Somalia a ranar jiya Lahadi.

Wani dan sanda da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bam din ya tashi ne a hanyar shiga ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar, inda ya ce, sun tabbatar da mutuwar mutane 5.

Wani ganau mai suna Mohammed Abdinasir, ya ce bam din ya fashe ne a wajen binciken ababen hawa dake gaban ma'aikatar kula da harkokin cikin gida.

Ya kara da cewa, 'yan sanda na binciken motoci da dama dake wajen a lokacin da bam din ya tashi.

Harin ya auku ne kasa da mako guda, bayan an kai wani mummunan hari a otel din Wehliye dake tsakiyar birnin, al'ammarin da ya yi sanadin rayuka 14.

Kawo yanzu dai, babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China