in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: Sin za ta yi kokarin tinkarar iftila'i
2018-05-12 15:39:53 cri
A yau Asabar ne, aka kaddamar da taro na musamman a birnin Chengdu na kasar Sin, domin tunawa da cika shekaru 10 da girgizar kasar da ta abku a gundumar Wenchuan dake yammacin kasar Sin, kana taron wani dandalin ne da aka shirya domin nazarin bala'in girgizar kasa inda kwararrun kasa da kasa suka hallarta. Bayan bude taron, shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping, shi ma ya aika da sakon taya murna ga masu shirya taron.

Cikin sakonsa, shugaba Xi Jinping ya ce, zuwa yanzu an samu nasarori sosai a kokarin sake gina ungwanin da bala'in girgizar kasar ya ritsa da su, har ma fasahohin da aka samu sun zama abin koyi ga kokarin tinkarar bala'i daga indallahi a nan gaba.

Shugaban na kasar Sin ya jaddada cewa, har kullum al'ummar duniya suna kokarin nazarin duniyarmu da muhallin dake kewaye da mu, tare da neman hanyar da za a bi wajen tinkatar bala'i daga indallahi. Muddin muna son mu biya bukatarmu a wannan fanni, akwai bukatar kasashe daban daban su hada kai tare domin gano dalilin da ke haddasa bala'i, da neman rage hadarin da ake fuskanta, da daidaita huldar dake tsakanin dan Adam da muhalli. A nata bangare, in ji shugaban, kasar Sin za ta tsaya kan manufarta ta ba da muhimmanci ga jama'ar kasa da kokarin magance barkewar bala'i, da kyautata fasahohin da ake amfani da su wajen tinkarar iftila'in.( Bello Wang )

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China